Kukan Kurciya: Yaushe Hausawa za su yi koyi da Maƙwabtan su?

Ɗazu I na-sauraren shirin rana na sashen Hausa na gidan radiyon BBC, na-jayo hirar da sun ka yi da Sarkin Yarabawan Ashanti ta ƙasar Ghana.

Daga Ɗankasawa gamida gyaran GobirMob

Abunda ya burge ni cikin hirar shi ne yanda ya yi maganar haɗin kai da zumunci da hulɗa ta arziki da ke tsakanin Yarabawan ƙasar, Musulmin su da Kiristocin su da masu bin addinin Gargajiyan su. Su na-ziyartar juna, su na-halartar bukukuwan juna, su na kuma yi ma juna jaje in abun jajen ya abku. Bambancin addini ba ya hana su hulɗa da cuɗanya da juna.

Saɓanin tsakanin mu Hausawa inda ƴan jahadi sun ka yi nasarar gina ƙatuwar katanga tsakanin Bahaushe Musulmi da Bahaushen da ba Musulmi ba. Katangar da ta kore mutumtaka da kyakkyawar hulɗa tsakanin Hausawa Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba na tsawon shekaru ɗari biyu da ɗoriya tun bayan jahadin Ɗanfodiyo.

Kowace ƙabila na hulɗar arziki da junan ta cikin natsuwa da kwanciyar hankali, amman Bahaushe Musulmi (musamman na Nijeriya) ya fi natsuwa ya yi hulɗa da Bayarabe Kirista ko Inyamuri da a ce ya yi hulɗa da ɗan uwan shi na jini Bahaushen da a ke kira “Bamaguje”. Tsakanin Bahaushe Musulmi da Bahaushen da ba musulmi ba, ba mutumci ba girmama juna. Daga ƙyamar juna sai gaba sai zargi sai cin duddugen juna. Haka Bahaushe zai dawwama?

Wannan illar shekara sama da ɗari biyu da an ka yi ma Hausawa za ta ɗauki lokaci mai tsawo nan gaba kafin Hausawa su gano ta balle su fara ƙoƙarin magance ta. Ina ma mu fara ganowa tun yanzu!

Mu na-fata dangi Hausawa su farka su gane cewa addinin Musulumci bai hana kyakkyawar hulɗa ba tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba, kuma kowace ƙabila, harda Larabawa, su na-cuɗanya da ƴan uwan su waɗanda ba musulmi ba bisa tafarkin “lakum dinikum wa liyaddini”.

Samo hanyar mutumta juna tsakanin Bahaushe Musulmi da Bahaushe Kirista da Bahaushen Bamaguje shi ne matakin farko na-daidaita gidan Malam Bahaushe da ke zama kara zube.

Mu ceto Hausa!

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post