Zanga-zanga: An kai Hamma Ahmadou gidan yari a garin Filingue

Labarai daga jamhoriyar Nijar na cewa an kai jagoran adawan ƙasar Hamma Ahmadou gidan yari, bayan ya miƙa kan shi ga ƴan sanda ranar Juma’a.

Kamar yanda BBCHausa ta ruwaito, wata majiya da ke da kusanci da Hamma Ahmadou ta tabbatar da tsare jagoran adawar na Nijar a gidan yari da ke garin Filingue.

Jaridar yaɗa labarai AFP ta ce an ɗarme Hamma Ahmadou bayan ya sha tambayoyi tsawon kwanakki ukku kan zargin shi da hannu a zanga-zangar da ta ɓarke bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda alƙaluma sun ka bada cewa Bazoum Muhammed ne ya lashe.

Ko da ya ke, zuwa yanzu hukumomi ba su ce komi ba gameda kamun na Hamma.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post