Ba mu fata: Lai Muhammad ya bayyana makomar masu kiran a raba ƙasa

Lai ya ce idan an raba Nijeriya gida biyu ko ukku Farfesa zai koma tallan burodi a ƙasashen waje.

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa, manyan mutane da sun ka kai matsayin Farfesa ya kamata su bar Tunzura mutane.

Ya ce yawancin matsalolin daga wajen irin waɗannan mutane su ke tasowa, ya ce da za ka je ƙauyukka. Za ka ga mutane na-zamne lafiya duk da bambancin ƙabilu ko addini.

Ya ce amman irin manyan mutane da ya kamata a ce su na-taimakawa wajen yaɗa aƙidar zaman lafiya, idan sun ka koma yaɗa ƙiyayya sai abu ya lalace, saboda yawancin mutane su na-sauraren su da tunanin cewa sun fi su sanin harkoki na rayuwa.

Ya ce yawancin su na-da takardun zaman ƙasashe (Passport) da yawa, kuma da an fara wani tashin hakali za su tsere su bar mutane cikin matsala. Ya ce amman fa su sani za su iya komawa aiki gidan burodi a ƙasashe irin su Togo, ya ce a baya an ga irin yanda hakan ta faru yayin da kasar Liberia ke fama da yaƙin basasa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post