Gurguwa Mai Tallan Ruwan Sanyi ta koma Kyakkyawar Gimbiya (Photos)

Gurguwa mai tallan ruwan sanyi ta sha kwalliya yayinda ta ke bikin cika shekaru ashirin da bakwai (27) da haihuwa. A watan Maris da ya gabata, duniyar yanar gizo ta fuskanci wata yarinya da ke yawon tallan ruwan sanyi a titin Birnin Lagos, duk da kasancewar ta gurguwa. Mary Daniels ta ba ma’abota kafofin sada zumunta tausayi sosai. Abunda ya faru da ita abun a tausaya ma ta ne, sannan makomar ta a yanzu abun a yaba ne, a kuma kwaikwaya.

Cikin ƴan kwanakki ta samu tarbacen kuɗi har miliyan goma sha-huɗu (14 million Naira).

Ƙarawa da ƙarau, Gwamnatin Jahar Lagos ta sanarda cewa ta ɗauke nauyin ƴar tallar da ita da ɗan ta guda ɗaya da uwar ta — wadda ta haife ta.

An kuma bayyana cewa Gwamnatin Jahar ta ba ta matsugunni kyauta dan kyautata ma rayuwar ta.

Yayinda ta ke bikin cika shekaru ashirin da bakwai (27) da haihuwa wasu masoya sun haska kamannin ta inda ta sha kyawo sosai, ba laifi.

GobirMob na-ma ta fatan alheri!
Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post