Olusegun Obasanjo ya yaba Gwamna Aminu Tambuwal yayinda ya aza Tubalin ginin Gadar Sama a Birnin Sokoto

Jiya Assabar, Chief Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar aiki ta kwana guda a Birnin Sokoto inda ya ƙaddamar da aza tubalin ginin Gadar Sama a Anguwar Rumjin Sambo wadda ke cikin Babban Birnin jahar Sokoto.

Olusegun Obasanjo wanda ya ƙaddamar da tubalin aikin gina gadar sama, ya samu rakkiyar Gwamnan Jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Sultan Abubakar Sa’ad, Sarkin Sokoto da sauran ƙusoshin Gwamnatin Jahar.

Sannan mun samu labarin cewa ya yaba ayukkan da Gwamnatin Aminu Waziru Tambuwal ke yi a faɗin jahar: birni da karkara. Ya faɗi hakan ne yayinda ya ke zantawa da ƴan jarida, sanda ya ke bankwana da su.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post