Shugaba Buhari ya sha alwashin yaƙi da Ƴan Ta'adda, ya jajanta ma Jami’ar Greenfield Kaduna

Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya yi Allah waddai da kashin ƴan makarantar Jami’ar Greenfield ta Kaduna su ukku (3) da ƴan ta’adda sun ka yi bayan sun kwashe ɗaruruwan ƴan makarantar dan neman kuɗin fansa. Buhari, ta bakin kakakin shi, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa wannan rashin imani ne da kuma ɗaukar alhaki duk da cewa a na cikin watan Azumi (Ramadan).

Yau Assabar Shugaban ya bayyana cewa, masu wannan abu ba za su samu Nasara ba. Ya ce Gwamnati za ta yi amfani da duk wani ƙarfin da ta ke da shi dan ganin ta yaƙi wannan ta’adi da su ke yi kusan kullum a Arewa-maso-yamma.

A saƙon da ya ɗora a kafar Twitter ya rubuta cewa:

Ina mai jajantawa iyalansu kuma Allah ya jikansu.

Wannan hare-hare da kashe-kashen dake faruwa, musamman a jihar Kaduna, abin takaici ne. Muna tabbatar da cewa zamu cigaba da yaki da dukkan yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk dukiyar da kasar nan ta mallaka.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post