Shugaba Buhari ya taya Aliko Dangote Murnar cika shekaru 64 da haihuwa

Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya taya Attajirin Africa, Aliko Dangote murnar cika shekaru 64 da haihuwa.

Ya bayyana haka ne ta bakin kakakin shi, Malam Garba Shehu. Shugaban ya ce, Dangote ya taimaka ma Nijeriya sosai wajen yaƙi da cutar coronavirus.

Ya kuma ce irin waɗannan ayyuka da ya ke na hidimtawa mutane, za su shiga tarihi wanda ƴan baya za su rinƙa tunowa da su.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post