Tsoho Shugaban Ƙasa Obasanjo ya kai ziyarar ban girma Fadar Masarautar Sokoto (Photos)

Tsohon Shugaban Ƙasa Chief Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a Sokoto inda tareda Gwamnan Sokoto Aminu Waziru Tambuwal ya kai gaisuwa fadar Mai Martaba Sarkin Sokoto, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar. Sun nuna damuwar su gameda ƙaruwar tashe-tashen hankula da kuma bambancin ra’ayoyi marar kyau tsakanin ƴan Nijeriya wanda hare-haren ta’addanci ya sanadar a ƙasar.

Ya ce taƙaddama tsakanin mabiya addinai dabam-dabam a kasar na-yin barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasar, inji Maimartaba.

Sarkin Sokoto ya kuma yi kira ga Olusegun Obasanjo da ya yi amfani da matsayin shi da sanin shi na addini (Theology) wajen haɗa kan mabiya Addinin Musulumci da Kiristanci wuri guda.

Kamannai daga ziyarar


Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post