Sokoto: Mutane sun yi Tarbacen Dubban Kuɗade dan fansar Garin su

Mutanen wani ƙauye a Jahar Sokoto
sun sun aika ma ƴan Bindiga Makuɗɗan Kuɗaɗe saboda gudun kar su kai musu farmaki.

Labarai sun tabbatar da cewar, mutanen Garin (Gidan Nashiyo) da ke ƙaramar
hukumar Illela wadda ke ƙarƙashin Jahar Sokoto sun hada kuɗi har Naira dubu ɗari biyu da hamsin (₦250,000) sun miƙa ma Fulani ƴan ta’adda dalilin sun ce da su
za su fatattake su matuƙar ba su bada
kuɗaɗen ba.

Tun da farin dai ƴan ta’addan sun shaida ma mutanen ƙauyen na Gidan Nashiyo cewar, su kai musu miliyoyin naira ko kuma duk su hallaka su.

To sai dai kuma mutanen kauyen sun yi
cinakin fansar garin su ga ƴan ta’addan
wanda tuni sun ka lamunce da karbar naira dubu ɗari biyu da hamsin (₦250,000).

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post