Sokoto: PDP ta gayyaci Ɗan Majalissar Dokoki, wanda ya yi kira kan Hare-haren Ta'addanci

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) reshen Jahar Sokoto ta aika ma ɗan Majalissar ta na dokoki takarda ta neman ƙarin bayani kan hirar da yayyi da Vision FM Sokoto, BBC Hausa, VOA Hausa inda ya faɗi cewa ya yi kiraye-kiraye ga Gwamnatin Tarayya da ta Jaha kan yaƙi da hare-haren ta’addanci a yankin shi a matsayin nauyin da ya rataya ga wuyan shi.

Ɗan Majalissar mai waƙiltar yankin Sabon Birni, Hon. Aminu Almustapha Boza, majiya ta bada cewa ya taba sayo ma Hukumar Ƴan Sanda ta Sabon Birni mota kirar Hilux ta Miliyan Takwas na Naira (N8,000,000) a matsayin ta shi gudummawa ga yaƙi da ta’addanci a garuruwan da ya ke jagoranta.

Amman dalilin kiran da PDP ta ma shi, kamar yanda ya bayyana a cikin rubutun takardar, sun maida hankali ne kan zancen da yayyi cewa zai iya aje muƙamin shi matsawar ba’a samu kwanciyar hankali a yankunan shi ba, saboda a cewar shi ya kai maƙura wajen faɗi tashi da kai komo dan ganin ya share ma mutanen yankin shi hawaye.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post