Sokoto: Sakamakon zaman Shugabannin PDP da Ɗan Majalissar Dokoki kan Yaƙi da Ta'addanci a Sabon Birni/Isa

Yau Talata, 25 ga watan Mayu na shekarar 2021 an ka gudanar da zama tsakanin Shugabannin Jam’iyyar PDP reshen Jahar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyya na Jaha, Alh Bello Aliyu Goronyo da kuma wasu Shugabannin ta da Hon. Aminu Almustapha Boza ɗan majalissar dokokin Jahar Sokoto mai waƙiltar Sabon Birni ta Arewa, zaman ya gudana a ɗakin taro na Shukura Hotel Sokoto da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

Jami’yyar PDP ta gayyaci Hon Aminu Boza ne bayan kiran da ya yi a kafafen yada labarai, inda Hon Aminu Boza ya shelanta aje kujerar shi ta ɗan Majalissar Dokokin Jahar Sokoto idan Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jaha ba ta ɗauki matakin da ya dace ba a kan Ƴan Ta’adda da sun ka addabi mutanen Sabon Birnin Gobir tsawon shekara biyu, su na-kashe mutane da sace dukiyoyin su, satar mutane da yi ma matan su fyaɗe ba dare ba rana, kullum abun sai ci gaba ya ke yi.

Hon. Aminu Almustapha ya yi ta kira a gaban zauren majalissar dokokin Jahar Sokoto da kafafen yada labarai na mummunan tashin hankalin rashin tsaro a karamar hukumar mulkin Sabon Birni babu wani mataki na a-zo-a-gani da Gwamnatoci sun ka dauka, yanzu haka adadi mai yawa na ƙauyukkan Sabon Birni sun watse inda mafi yawa sun ka yi gudun hijira zuwa ƙasar Nijar dan su tseratar da rayukkan su.

Zaman ya gudana, inda jami’yyar PDP ta ke tambayar Hon. Aminu Almustapha Boza dalilin shi na furta wannan kalamin da ke nuna gazawar Gwamnatin ta bangaren tsaro, kamar yanda sun ka ce Gwamnatin Jahar Sokoto ta na iyakacin ƙoƙarin ta dan samar da tsaro a Jahar.

Hon. Aminu Boza ya tabbatar ma kwamiti halin da yankin shi ya ke ciki inda a lokacin zaman ya ke amsa kiran waya da a ke sanar da shi ƴan ta’adda sun kashe Maigarin Magira a yankin Gatawa, ya kuma sanar da kwamitin ƙoƙarin da ya ke yi ta bangaren tsaro, daga lokacin da an ka rantsar da shi zuwa yau ya kashe kuɗi kimanin naira miliyan ashirin da hudu (₦24,000,000) ciki harda mota kirar Toyota Hilux da ya sayo ma Ƴan Sanda.
Hon. Aminu Boza ya tabbatar da ba za shi razana ba kuma ba za shi sauya matsayar shi ba idan Gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba a wannan mummunan halin da mutanen da ya ke jagoranta su ke ciki. Babu amfanin zaman shi waƙilin mutanen da Gwamnati ta wofintar a na ta kashe su a na-cin zarafin mata a na-kwashe ma su dukiya. Yanzu damuna ta kama talakkawa ba su da kwanciyar hankalin da za su yi noma su samu abunci, babu tallafi ga ƴan gudun hijira da sun ka baro matsugunnan su.

A ƙarshen zaman an samu kyakkyawar ganawa da gano bakin zaren inda matsalar ta ke. Mutanen yankin Sabon Birni sun aje bambancin jam’iyya su na ta adduo’in fatan alhairi da kariyar Allah ga Hon. Aminu Almustapha Boza ga ƙoƙarin da ya ke yi a bangaren tsaro da jin dadin mutanen da ya ke jagoranta.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post