Tirƙashi: Wani Bakatsine ya sauya sheƙa zuwa Bagobiri

Kamar da wasa wani mutum mai suna Mati wanda Bakatsine ne asali ya bada kan shi ga wanzami ya ma shi tsagen Gobirawa ga fuska kan zunzurutun kuɗin CFA har jikka ɗari biyar (500,000 cfa). Labarin ya faru ne a wani gari da ke cikin Jahar Maradi, Jamhoriyar Nijar.

Mati abokin wasa ne ga wasu gungun Gobirawa kamar kullum, kun sa wasan tabbashintaka tsakanin Gobirawa da Katsinawa. Tarihi ya nuna Gobirawa da Katsinawa dangin juna ne kuma maƙwabtan juna ne, masana sun ce Gobirawa su ke ɗan namiji, Katsinawa kuma ɗiyan macce. Saboda haka wasa tsakanin waɗanga gungun Hausawa biyu ta yi ƙamari ta ɗore, kamar irin wasar da ke tsakanin Kanawa da Zazzagawa, Barebari (Kanuri) da Fulani, da sauran su.

A na cikin irin wannan wasa wata rana Mati Bakatsine ya ce ma Gobirawa da ke wasa da shi idan sun isa su maida shi Bagobiri. Shi kuma Nura Andume wanda Bagobiri ne, ya saye zancen ya ce ma Mati, “Nawa ne Katsinancin na shi ya ke?”, ya ce jikka ɗari biyar (500,000cfa). Da wasa da wasa Nura ya kawo kuɗi ya hannanta ma Bakatsine, Bakatsine ya ga kuɗi, ya saida Katsinanci, ya koma Bagobiri.

Ganin kar garaɓasa ta wuce shi ya bada kai wanzami ya mishi tsagen Gobarci, nan-shidda (6) nan-bakwai (7) kuma ya ce daga yanzu duk wanda ya ƙara kiran shi Bakatsine shi da shi. Shi kuma Nura Andume ya ce duk haihuwar da an ka ma Mati ya ɗauke nauyin rago, kuma za’a yi ma jaririn ko jaririyar tsagen Gobirawa (shatune guda biyu) a fuska.

An ce Mati uban shi Bakatsine ne, uwar shi kuma Bagobira. Bisa ƙa’idar dangantaka har yanzu Mati Bakatsine ne duk da sauyin sheƙar da yacce ya yi.

Gobirawa sun shammace shi. Bakatsine an ga kuɗi!

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post