Za'a fara ƙera Wayoyin Zamani da Layukka a Nijeriya – Pantami

Ministan Sadarwa na Nijeriya Dr. Isa Ali Pantami ya ce ƙasar Nijeriya na-da damar da za ta samar da layukkan wayar salula watau SIM cards da kuma wayoyin hannu na zamani (Smart Phones) dan cigaban kasuwancin su a nahiyar Afirka.

Pantami ya bayyana haka ne yayin wani taro da wata majallisar ƴan jam’iyyar APC mai mulki ta shirya a Abuja ranar Alhamis, kamar yanda kafar labarai ta BBC Hausa ta ruwaito.

Majalissar ta shirya taron ne ga ministocin gwamnati dan bayyana ayyukan da su ke gudanarwa a ma’aikatun su.

Da ya ke bayani a wurin taron, Pantami ya ce nan gaba kaɗan za a bar shigar da kashi 60 zuwa 70 na kayayyakin da a ke amfani da su a ɓangaren sadarwa zuwa Nijeriya daga ƙasashen waje.

Ya ce ƙasar na da ƙarfin da za ta iya samar da layin waya miliyan ɗari biyu (200,000,000) a duk shekara.

“Mun samar da wani tsari na ƙera aƙalla kashi 60 zuwa 70 na abubuwan da mu ke buƙata a ɓangaren sadarwa nan da shekara biyu ko ukku saboda za mu fara ƙera su a cikin gida, kuma har mun fara,” in ji shi.

“Lokacin da gwamnatin nan ta hau mulki, hatta layukkan salula sai an shigo da su daga ƙasar waje. Yanzu gwamnati ta samar da yanayin da a ke iya samar da su da kuma ƙera wayar salula ta zamani ba wai kawai dan amfanin cikin gida ba, har da nahiyar Afika.

“Yanzu haka a Najeriya, mu na-ƙera wayoyin salula na zamani.”

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post