Fadar Masarautar Kabi mai ɗimbin Tarihi (Photos)

Tsohuwar fadar Masarautar Kabin Argungu wadda yanzu ta koma wajen ajiyar kayan tarihi ta ƙasa watau National Monument. An laƙaba ma ta suna Kanta Musuem kamar yanda bayanai sun ka bada. A cikin garin Argungu ta ke na Jahar Kebbi.

Ma’adanar kayan tarihin ta samo sunan ta ne daga tsohon Sarkin Kabi Muhammadu Kanta (1517 – 1561), wanda tarihi ya bayyana a matsayin Malami kuma gwanin iya yaƙi.

Kabawa na daga ɗayan rukunnan ƙabilar Hausa su guda goma sha-shidda (16). Za ku iya samu Kabawa a ko’ina a ƙasar Hausa, Nijeriya da Nijar. Kamar dangin su Gobirawa, Kabawa mutane ne da sun ka yi fice wajen yaƙi. Sun kare yawancin masana’antun su daga faɗawa mulkin mallakar Fulani a zamanin yaƙin Usman Danfodio (1804). Kabawa har yanzu cikin shirin yaƙi su ke, ta bakin wani Mawakin Hausa.

An san su da sana’ar kamun kifi wadda ta sanadiyyar haka ta haifar da gasar kamun kifi ta duniya (Argungu International Fishing Festival) wadda ke gudana a garin Argungu da ke Jahar Kebbi.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post