Ihun Kaduna: Shugaba Buhari ya ga Ishara babba jiya

Kamar yanda Hausawa ke cewa “komi nisan dare gari zai waye”, kuma “gaskiya kaɗai ke dawwama”. Lallai sai yau mun ka ƙara sanin waɗannan salon magana na Hausawa. A ce yau an wayi gari wanda a ke yi ma wasu ihu saboda shi yau shi a ke ma ihu, wanda a ke jifan wasu saboda shi yau shi a ke jifa, wanda a ke ƙone-ƙone saboda shi yau shi a ke ƙona hotunan shi. Har wasu na Allah ya isa, ba mu yafe ba, kun ci amanar mu.

Shin anya kau Buharin da mun ka sani ne? Mi ke faruwa? Mutane sun dawo daga rakkiyar shi kenan?

Ko shakka babu idan ka yi bincike kan abubuwan da ke faruwa a yau za ka gane cewa yanda miliyoyin ƴan Nijeriya sun ka ƙosa da irin kamun ludayin Buhari. Mutune na cike da fushi duk da kokarin gwamnati na ɓoye abunda ke faruwa.

Mi ya sa haka?

Daga 2003 har zuwa 2015, Allah kaɗai ya san adadin ƴan Arewa da sun ka rasa rayukkan su kan lallai sai Buhari ya yi mulki. A zaɓukkan 2015, sama da mutum 40 sun rasa rayukkan su a yankuna da dama na Nijeriya dan murnar ganin an zaɓi mai gaskiya. Mutane sun sadaukar da rayuwar su wajen ganin sai shi mai adalci ya ci.

Sai kwatsam ga baba mai gaskiya ya hau mulki, sai kwatsam ya sauya kama. Wanda ƴan Nijeriya ke yi ma kallon Mahadi mai ceto, Sai ga shi ya zamo musu kamar mugun sarki. Wasu sun zaci a sabon wa’adin mulkin shi zai sauya, amman ina? Ba a Kaduna kadai a ke yi ma Buhari ihu ba, har a Borno, Zamfara da Katsina dss.

Dalilan su ne kamar haka:

1. Harakar tsaro: sau tarin yawa ba abunda Buhari ke yi da ya wuce Allah waddai. Daga 2015, shekarar hawan mulkin shi zuwa yanzu, an kashe aƙalla mutum 6000 a Arewa-maso-yamma. Ƴan Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna da Niger sun yi kukan jini. Buhari ko jaje bai taɓa zuwa ba. Hasali ma sai da ya hau kujerar na-ƙi kan ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda. Wannan ya ba mutanen Arewa mamaki da baƙin ciki yanda Buhari ya zura ma ƴan ta’adda idanu, ya bar su su na-kashe-kashe, ƙone-kone, yanda sun ka ga dama, ba tare da yace ƙanzil ba. Kowa ya san ba su fi ƙarfin gwamnati ba. Idan kun tuna, shi da kan shi kafin ya hau mulki ya ce babu ƴan ta’adda da za su gagari gwamnati, sai dai in an ƙyale su. Na yarda da maganar ka Shugaba Buhari, ƙyale su an ka yi.

2. Abu na biyu shi ne tsadar rayuwa. Duk yanda gwamnati mai mulki ta ke ƙoƙarin ɓoye gazawar Buhari kan tsadar rayuwa, bai hana kowa ya san gaskiyar mi ke faruwa. Tsadar abunci, tsadar man fetur, tsadar tsamin zamani da sauran su.

A ƙarshe, akwai tabbacin cewa duk fushin da ƴan Kaduna sun ka yi wanda ya sa sun ka yi ma Buhari ihu da Allah ya isa, bai kai kwatamkwacin na mutanen yankin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kebbi ba. Saboda a ƙarƙashin mulkin Buhari ne an ka kore su daga gidajen su, an ka ƙone musu amfanin gona da gidaje. Yau wasun su na ƙasar Nijar ga hannun Allah. Akwai tabbacin za su yi ma Buhari abunda ya fi wanda an ka yi ma shi jiya a Kaduna. Dama kawai suke jira.

Lallai duk abunda mutum ya shibka, shi zai girba. Nan zuwa yyan kwanakki, zai sabka daga karagar mulki ba tare da ya cika alƙawarin da ya yi ma mutane na kare rayukka ba tsawon shekaru takwas (8). Ruwa dai ya ƙare ma ɗan kada.

Sauran hukumci kuma mu jira mu gani.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post