Manyan Nasarori 10 da Hausawa Ƴan gwagwarmaya sun ka samu a Shekarar 2021

Hausawa na cewa sannu ba ta hana kaiwa, sai dai a jima ba a kai ba. Kowa ya san a na-yi ma Hausawa kallon waɗanda ba su da kishin kan su, ga kuma sakaci a ɓangaren neman mulki da wasu ɓangarori na rayuwa wanda ya baiwa wasu damar ɗarewa har a yankunan da Hausawan ne ke da gagarumin rinjaye. Wannan gaskiya ne, Bahaushe dakwai sakaci, rashin kishin na shi. Tau sai dai bai dace mu kau da idanun mu ga cigaban da an ka samun cikin ƙanƙanin lokaci ba. Wannan ya samu ne albarkacin ƴan gwagwarmayar Hausa yawanci a kafofin sada zumunta na zamani.

Nasarorin su ne kamar haka:

1. Tabbatar da kasancewar ƙabilar Hausa

Masu mulkin mallaka sun yi amfani da wani babban makami dan ƙara DURƘUSAR da Hausa ta hanyar kore samuwar ƙabilar kwata-kwata a doron ƙasar Hausa. An yi lokuta a baya idan ka ce kai Bahaushe ne, sai Fulani ƴan mulkin mallaka su ce ma ka ai Hausa yare ne ba ƙabila ba. Tau amman yau da kan su sun dawo daga wannan shirmen. Hausa ƙabila ce, yare ne kuma tabi’a ce.

2. Fayyace masu ta’addanci da masu amfani da harshen Hausa

Masu gwagwarmayar Hausa sun yi iya ƙoƙarin sanar da duniya kan cewa ba wai dan Shekau ko Bello Turji ko wane na magana da harshen Hausa ba ne ya ke kasancewa Bahaushe. A’a, mafi yawan su su na-amfani ne kawai da harshen Hausa amman su na-da ƙabilun su. Ƙasashen duniya da dama sun zaci ai duk waɗannan ƴan ta’addan Hausawa ne. Sai yanzu da an ka samu marubuta na yamar gizo da su ke raba tsananin zare da abawa. Sai an ka gano ashe duk yan ta’addan babu Bahaushe ko ɗaya a ciki.

3. Tona asirin masu ci da gumin Hausa

Cikin ƙanƙanin lokaci, masu gwagwarmaya sun nuna dalla-dalla yanda a ke amfani da sunan Arewa da kuma Addini a na-ci da gumin Hausawa. Wannan ya sa na gane cewa ashe yawancin masu kiran kan su dattawan Arewa ashe ba Hausawa ba ne, ashe ma ƙabilar su su ke karewa ba Arewa ba. Misalin da Ango Abdullahi da ya ce wai a na-zaluntar Fulani ya kuma yi kira da a ɗauki mataki. Wannan ya ba mu damar gano zunzurutun munafurcin da a ke yi kan Malam Bahaushe.

4. Zaburar da Hausawa

Wani abun ban sha’awa kan ƙoƙarin da ƴan gwagwarmayar zamani na Hausa sun ka yi shi ne, zaburar da Malam bahaushe kan ƙalubalen da ke gaban shi. A lokutan baya, da wuya ka samu mutum ya buga kirji a kafofin sada zumunta ya ce shi Bahaushe ne ballantana ma ya yi sha’awar magana kan Hausa. Amman yau sai ga shi ɗaruruwan mutane daga cikin su har da Malaman jami’o’i Hausawa sun karbi wanga ra’ayi na Hausanci (Hausahood).

5. Maida hankali kan tarihin Hausawa

A karo na farko an samu marubuta Hausawa masana ciki da wajen Nijeriya da sun ka ƙaryata tarihin kanzon kurege na Hausa da masu mulkin mallaka sun ka rubuta. Da yawa sun gano cewa mafi yawan littafai da an ka rubuta kan Hausa a baya, ko dai Fulani ne sun ka rubutu su ko kuma Fulani sun ka sa a rubuta dan su kare yaƙi da mamayar da sun ka yi ma rabin ƙasar Hausa. Da yawa sun gano cewa Sarakunan Hausa na dauri da Fulani sun ka yaƙa ashe duk musulmai ne kamar su Sarki Kano Muhammadu Alwali, Sarkin Kabi Muhammadu Kanta, Sarki Zazzau Muhammadu Makau, Sarkin Gobir Muhammadu Yumfa, Sarkin Katsina Muhammadu Korau da dai sauran su.

6. Fallasa muyagun manufofin kan ƙasar Hausa

Ya na daga cikin abunda mun ka gano, cewa akwai ɓoyayyar manufa kan Ƙasar Hausa da wasu maƙiya ke yi. Wannan manufa ta haɗa da kashe mutane dan a rage yawan su, da kuma karɓe ikon duk wasu yankuna masu albarkatun ƙasa kamar su Zamfara, Katsina dss. A da ba mu san haka na, mun dauka kawai ƴan garkuwa ne (Kidnappers), ashe akwai wata munakisar da su ke tasawa.

7. Sabon tsarin siyasar Ƙasar Hausa

Sai a waɗanga lokuta mun ka ga cewa ya dace Bahaushe ya tashi ya yi ƙoƙarin kare mutumcin shi ta hanyar neman muƙamai na siyasa da kare masarautun Hausa na gargajiya. Dole ne masarautu irin su Zazzaun Suleja, Sabon Birnin Gobir, Kabin Argungu dss su samu daraja ta ɗaya.

8. Matsin lamba ga gwamnatin Shugaba Buhari

Ko shakka babu gwamnatin Buhari ba ta yi niyyar ayyana masu garkuwa a matsayin ƴan ta’adda ba duk da munin ta’addancin su. Amman daga ƙarshen watan Disamba zuwa makon farko na Janairu, mun ga yanda dandazon masu kare hakkin talakkawa sun ka yi zanga-zanga ga gwamati kan lalle masu garkuwa da mutane sun aikata ta’addanci mafi muni. Abun mamaki ma shi ne har da hotuna da sunayen kwamandodin yan ta’adda mun gani wasu sun fitar. A ƙarshe dai gwamnatin ta ga babu makawa, dole ta ayyana su a matsayin yan ta’adda. Nasara kenan!

9. Haɗin kan Hausawa

Tun daga karni na 19 zuwa yanzu, ba a taɓa lokacin da Hausawa sun ka ga muhimmancin haɗin kai ba irin wanga. Hausawa sun ka gane cewa tsira da mutumci zai samu ne kawai idan sun hada kan su. Gobirawa, Kanawa, Zazzagawa, Kabawa, Zamfarawa dss. Har yau ga shi an samu wasu ƙungiyoyi na Hausawa tsantsa masu kare muradun Hausa. Wannan albarkacin wagga gwagwarmayar ne.

10. Firgita azzalumai

Abu na goma. Ƴan gwagwarmaya sun motsa ƙasa, sun tayar da ruwa. An ka wayi gari azzalumai na ɓoye sun ka fito fili.

@Ali Garba Bahaushe

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post